Warri
Warri | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jihohin Najeriya | jahar Delta | |||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci | ||||
Wasu abun | ||||
| ||||
Yanar gizo | deltastate.gov.ng |
Warri birni ne, da ke a jihar Delta, a Najeriya. Shi ne babban birnin jihar Delta. Bisa ga kimanta a shekarar 2017, jimilar mutane dubu dari shida da sittin da uku. Birnin Warri cibiya ne na man-fetur da ke kudu-maso-kudancin kasannan, kuma gidan gwamnati na Jihar Delta na cikinta. Itace matsayin yankin gundumar Turawan Mulkin mallaka na lokacin.[1]
Warri ta hada yanki da Sapele, duk da cewa a yanzu an hade yankunan Sapele kamar su Okere, Agbassa, Uvwie, Okpe, da kuma Udu a matsayin yankin babban Birnin Warri.[2] Akwai gidajen Osubi da filin jirgin sama guda daya a garin.
Kalmar "Gundumar Warri" a da tana nufin wani yanki na jihar Delta, wanda ke karkashin mulkin turawa na yankin Kudancin Najeriya.[3] Ta hada yanki da Sapele daga Arewa-maso-Gabas, da kuma Rafin Forcados daga Kudu-maso-Gabas, sai kuma Jameson Creek daga kudu-maso-yamma wanda daga baya ta koma karkashin gundumar Delta. Effurun itace matsayin cibiyar tattalin arzikin birnin.[4]
Birnin Warri tana daya daga cikin maya-manyan cibiyoyi sarrafa da kuma kasuwancin man-fetur dake kudancin Najeriya. Itace babban birnin kuma cibiyar kasuwanci na jihar Delta, da yawan mutane akalla mutum 311,970 dangane da kidayar shekara ta 2006.[5]
Asalin mazauna birnin sun kasance mutanen harsunan Urhobo, Ijaw da Itsekiri. Sannan mafi aksarin mazauna garin kiristoci ne, duk da dai har yanzu akwai kadan dake bin akidar bautan gargajiya na kudancin Najeriya. Birnin tayi fice a harshen Turancin Pijin (Pidjin English).
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]Warri a da ta kasance babban birnin gundumar mulkin Turawa. Daga bisani an hade Lagos da Yankin Kudancin Najeriya a matsayin yankunan mulkin mallakan Turawa a ranar 28 ga watan February 1906, kuma an daura Walter Egerton a matsayin gwamnan yankin wanda ya rike mukamin har zuwa 1912.
Birnin Warri na nan a gaban kogin Warri wacce ta hade kogin Forcados da na Escravos ta Jones Creek a can yankin Delta. Tarihin garin ya fara ne a karni na 15 lokacin da malaman kiristoci daga Portugal suka kawo masu ziyara. Daga baya kuma ta zamo cibiyar cinikayyar bayi tsankanin Portugal da Germany. Warri ta zamo birni mai daraja a karni na 19 musamman ta dalilin tashan jirgin ruwa da ake sufurin man-ja zuwa kasashen ketare.
Sannan Warri ta zamo cibiyar gundumomi na Turawa a karni na 20. Ta samu cigaba sosai, ta tashi daga kauye ta zamo birni.[6]
Jama'a
[gyara sashe | gyara masomin]Mafi akasarin mutanen warri sun kasance daga harsunan Urhobo, Itsekiri da kuma Ijaw.[7] Amma saboda bunkasa da cigaban garin, akwai mutane dayawa daga sassa daban daban na kasar.
Yanayi
[gyara sashe | gyara masomin]Birnin na fuskantar matsakaicin ruwan sama da kuma matsakaicin danshi. Yanayin garin ya fada a monsoon wanda ya rabu zuwa yanayi biyu; lokacin damuna da lokacin rani. Rani yakan fara a tsakanin watan Nuwamba zuwa April kuma ya kunshi yanayin sanyin harmattan mai zuwa da kura da hazo. Lokacin damunan yana farawa ne daga watan Mayu zuwa October da rashin ruwa na dan lokaci acikin watan Augusta. Yanayin garin na da halayyar tropical monsoon climate da matsakaicin zafi na shekara-shekara a 32.8 °C (91.0 °F). Ruwan sama a shekara yakan kai 2,770 mm (109 in). Yanayi na zafi yakan kai 28 °C (82 °F) and 32 °C (90 °F). Kasan garin na dauke da isassun ciyayi, sannan akwai itacen timber, Palm da sauran itacen marmari.
Climate data for Warri | |||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Watan | Janairu | Fabrairu | Maris | Afrilu | Mayu | Yuni | Yuli | Ogusta | Satumba | Oktoba | Nuwamba | Disamba | Shekara |
Average high °C (°F) | 31.5 (88.7) |
32.2 (90.0) |
32.4 (90.3) |
32.2 (90.0) |
31.5 (88.7) |
30.0 (86.0) |
28.4 (83.1) |
28.4 (83.1) |
28.8 (83.8) |
30.0 (86.0) |
31.4 (88.5) |
31.5 (88.7) |
30.7 (87.3) |
Daily mean °C (°F) | 26.8 (80.2) |
27.5 (81.5) |
27.9 (82.2) |
28.0 (82.4) |
27.3 (81.1) |
26.3 (79.3) |
25.2 (77.4) |
25.3 (77.5) |
25.5 (77.9) |
26.3 (79.3) |
27.1 (80.8) |
26.8 (80.2) |
26.7 (80.1) |
Average low °C (°F) | 22.1 (71.8) |
22.9 (73.2) |
23.5 (74.3) |
23.8 (74.8) |
23.1 (73.6) |
22.6 (72.7) |
21.0 (69.8) |
22.3 (72.1) |
22.3 (72.1) |
22.6 (72.7) |
22.9 (73.2) |
22.2 (72.0) |
22.6 (72.7) |
Average precipitation mm (inches) | 30 (1.2) |
58 (2.3) |
127 (5.0) |
201 (7.9) |
270 (10.6) |
367 (14.4) |
474 (18.7) |
324 (12.8) |
457 (18.0) |
325 (12.8) |
104 (4.1) |
31 (1.2) |
2,768 (109.0) |
Source: Climate-Data.Org[8] |
Arziki da gine-gine
[gyara sashe | gyara masomin]Akwai Warri Refinery da kuma Petrochemicals a Ekpa, da sauran kamfanonin mai na gida da na kasashen waje a sassa daban daban da ke kusa. Tana daya daga cikin manya manyan tashoshi jiragen ruwa na Najeriya wanda ke nan a Ugbuwangue, Warri.
Saboda rikicin da ke faruwa a yankin, musamman na 1999, mafi yawanci kamfanonin sun ruga zuwa babban birnin da kuma sassan gefe-gefe.
Tsaro
[gyara sashe | gyara masomin]Akwai barikin sojoji a garin Amphibious Infantry battalion (Effurun Army Base) wanda ke nan a Effurun.
Sojin ruwan Najeriya suna gudanar da harkokinsu a yankin tashar. Sannan har wayau sojin saman Najeria na da bariki a garin (61 Nigerian Air force).
Wasanni
[gyara sashe | gyara masomin]Warri na da filin wasannin kwallon kafa wanda ke da fadin dibar mutane 30,000. Wanda shine filin wasan kungiyar kwallon kafa na gida na Warri Wolves.[9][10]
Sarrafe-sarrafe
[gyara sashe | gyara masomin]A cikin birin akwai manya manyan matatun man fetur, sannan akwai kamfanin sarrafe karafa watau Delta Steel Company wanda kenan a yankin Ovwian–Aladja dake karamar hukumar Udu[11]. Sanna akwai kamfanin sarrafa gilasai na Beta Glass daga wajen birnin Ughelli, wanda ke da tarin silica da silicates da ake amfani dasu wajen hada gilasai. Sannan har wayau akwai kamfanin rarraba wutar lantarki na Transcorp Power wanda kenan a Ughelli.
Sufuri
[gyara sashe | gyara masomin]Jirgin kasa
[gyara sashe | gyara masomin]A farkon shekara ta 1991, an fara hada titin jirgin kasan daga kamfanonin sarrafa karafa na Ajaokuta zuwa tashar jirgin ruwa na Warri wanda ke da nisan kiloitoci 275. Zuwa shekara ta 2006, titin jirgin ya kai kilomita 329 amma har yanzu ba'a kammala sauran kilomita 27 da ya rage zuwa Warri ba. An cigaba da aikin titin a shekara ta 2010. Gwamnati tayi bikin bude titin a watan Satumba shekara ta 2020.
Tituna
[gyara sashe | gyara masomin]Gwamnatin garin ta kara gyara manyan hanyoyin garin don kara wa garin kyawu.
Jirgin Sama
[gyara sashe | gyara masomin]Akwai wuraren saukan helikoptoci a wasu manyan kamfanonin man fetur a garin
Jiragen Ruwa
[gyara sashe | gyara masomin]Sufurin kayayyaki ta ruwa na gudana ne karkashin kulawar Nigerian Ports Authority (Delta Ports) wanda yawanci ya kunshi shigowa da kaya da fitasu daga wasun manyan kamfanoni.
Wuraren Ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]Jami'oi
[gyara sashe | gyara masomin]Akwai manyan makarantun gaba da sakandare da dama da suka hada da;
- College of Education at Edjeba, Warri[12]
- The Delta State Nursing School, Ogunu, Warri[13]
- Eagle Heights University, Omadino, Warri[14]
- Nigeria Maritime University Okerenkoko, Warri[15]
Makarantun Sakandare
[gyara sashe | gyara masomin]Makarantun Sakandare sun hada da:
- Yonwuren Secondary School, Warri
- College of Education Demonstration Secondary School, Warri
- Twin Fountain Group of Schools
- Cambridge International School
- Delta Careers College
- Federal Government College
- Hussey College, Warri
- Nana College, Warri
- Dom Domingos College, Warri
- Delta Secondary School, Warri
- Dore Numa College, Warri
- Essi College, Warri
- Uwangue College, Warri
- Urhobo College, Effurun
- Classical International Schools
- Ugborikoko Secondary School
- Army Day Secondary School, Effurun
- College of Commerce Warri
- DSC Technical High School, Ovwian-Aladja
- Our Lady's High School, Effurun
- Mega Stars Christian School, Udu
- Eagles Height School, Ajamhimogha
Makarantun firamare
[gyara sashe | gyara masomin]Makarantun firamare sun hada da:
- Ogiame Primary School, Warri
- Ikengbuwa Primary School, Warri
- Cavagina Primary School, Warri
- Twin Fountain Group of Schools
- HillTop
- International Unity School (IUS)
- NNPC Staff Primary School
- SNAPS
- Alderstown School for the Deaf
- Kids Compute Academy
Wuraren bude ido
[gyara sashe | gyara masomin]Akwai wuraren bude ido da dama da mutum zai iya ziyarta a Warri.
- Nana Living History Museum[16]
- Red Mangrove swamp
- Falcorp Mangrove Park / Mini Zoo, Ijala, Behind Warri Refinery.[17]
- Warri Township Stadium[18]
- Shell club, Ogunu[19]
Shahararrun mutanen
[gyara sashe | gyara masomin]- Isaiah Ogedegbe, faston kuma marubuci[20]
- Paul Eyefian
- Daniel Dikeji Miyerijesu shi ne ya kafa ma' aikatar Alheri ta Allah
- Ifeanyi Palmer shi ne ya kafa Gospel Harvest Assembly (Word Arena)
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Warri, Nigeria – International Cities of Peace". Retrieved 25 June 2021.
- ↑ "GPS coordinates of Warri, Nigeria, DMS, UTM, GeoHash - CountryCoordinate.com". www.countrycoordinate.com. Retrieved 25 June 2021.
- ↑ Okoh, Oghenetoja (July 2016). "WHO CONTROLS WARRI? HOW ETHNICITY BECAME VOLATILE IN THE WESTERN NIGER DELTA (1928–52)*". The Journal of African History. 57 (2): 209–230. doi:10.1017/S0021853716000074. ISSN 0021-8537. S2CID 163543228.
- ↑ "Exposure assessment of chicken meat to heavy metals and bacterial contaminations in Warri metropolis, Nigeria". ResearchGate. Retrieved 12 September 2021.
- ↑ "Archived copy" (PDF). Archived from the original (PDF) on 24 September 2015. Retrieved 5 June 2013.
- ↑ Ekeh, Peter Palmer (2005). Warri City and British Colonial Rule in Western Niger Delta. Urhobo Historical Society. p. 31. ISBN 978-064-924-7.
- ↑ "Niger Delta moving from agitation to rebellion?". The New Humanitarian (in French). 8 July 2003. Retrieved 25 June 2021.
- ↑ "Climate: Warri". Climate-Data.org. Retrieved 29 October 2016.
- ↑ Warri Wolves F.C
- ↑ Warri Township Stadium
- ↑ "20 years after collapse, steel company resumes operations". Vanguard (Nigeria). 5 March 2018. Retrieved 21 March 2018.
- ↑ "Contact Us – College of Education, Warri" (in Turanci). Retrieved 2021-06-25.
- ↑ "Delta State Schools of Nursing Admission Form 2020/2021". www.myschoolgist.com (in Turanci). 2021-02-26. Retrieved 2021-06-25.
- ↑ "How Oritsejafor Will Bankroll N2.5 billion Eagle Height University | Encomium Magazine" (in Turanci). Retrieved 2021-06-25.
- ↑ "Homepage". NMU (in Turanci). 2018-06-11. Retrieved 2021-06-25.
- ↑ "100 years of Nanna of Itsekiri's 'Living History'". Vanguard News (in Turanci). 2016-07-09. Retrieved 2021-06-25.
- ↑ "Opening hours: Falcorp Mangrove Park - Warri Zoo and Nature Park". opening-hours.com.ng (in Turanci). Retrieved 2021-06-25.
- ↑ "Warri Township Stadium - Football Stadium". Football-Lineups. Retrieved 2021-06-25.
- ↑ "Shell Ogunu Golf Club | All Square Golf". www.allsquaregolf.com (in Turanci). Retrieved 2021-06-25.
- ↑ "Iginla, TeeMac, others eulogise TB Joshua at posthumous birthday". The Nation Newspaper. Archived from the original on 2023-06-13. Retrieved 2023-06-20.CS1 maint: BOT: original-url status unknown (link)