Jump to content

Gregory Ngaji

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Gregory Ngaji
mutum
Bayanai
Jinsi namiji
Ƙasar asali Najeriya
Suna Gregory
Shekarun haihuwa 17 Nuwamba, 1946
Yarinya/yaro Jude Ngaji (en) Fassara
Sana'a ɗan siyasa
Muƙamin da ya riƙe mamba a majalisar dattijai ta Najeriya da mamba a majalisar dattijai ta Najeriya
Ilimi a Jami'ar Najeriya, Nsukka
Ɗan bangaren siyasa Peoples Democratic Party

Gregory Ngaji ɗan siyasar Najeriya ne wanda ya taɓa zama ɗan majalisar dattawa ta ƙasa mai wakiltar mazaɓar Cross River ta Arewa a jihar Cross River tsakanin shekarar 2003 zuwa 2011.[1]

An haifi Gregory Ngaji a ranar 17 ga watan Nuwamban 1946. Ya halarci Kwalejin Mary Knoll, Okuku, Yala, Jihar Cross Rivers, daga 1961 zuwa 1965, ya sami LL. B, daga Jami'ar Nigeria, Nsukka, a cikin shekara ta 1977, kuma ya sami BL daga Makarantar Shari'a ta Najeriya a cikin shekara ta 1978. Kafin a zaɓe shi a majalisar dattawa, ya kasance shugaban ƙaramar hukumar Yala, kuma ya taɓa zama memba a taron tsarin mulki daga 1994 zuwa 1995).[1]

Aikin majalisar dattawa

[gyara sashe | gyara masomin]
Jihar Cross River a Najeriya

A matsayin ɗan takarar jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), Gregory Ngaji an zaɓe shi a matsayin sanata a majalisar wakilai ta ƙasa mai wakiltar Kuros Riba ta Arewa a 5 (2003-2007), kuma an sake zaɓen shi a cikin watan Afrilun 2007. Yana aiki a kwamitoci akan Albarkatun Ruwa, Kimiyya da Fasaha, Sufurin Ruwa, Magungunan Narcotics Anti Corruption and Agriculture[1]

Ya kasance mamba a kwamitin majalisar dattijai da ya tantance Misis Farida Waziri a cikin watan Yunin 2008 domin neman muƙamin shugabar hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa ta EFCC.[2] A cikin watan Afrilun 2009, yana ɗaya daga cikin waɗanda suka ɗauki nauyin ƙudirin kafa Hukumar Sufuri ta Najeriya don maye gurbin Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ruwa ta Najeriya.[3] A wani nazari na tsakiyar wa’adi na Sanatocin Najeriya da jaridar This Day ta buga, jaridar ta lura cewa Ngaji ya ɗauki nauyin kudirin hukumar binciken sararin samaniya ta ƙasa, 2008, kuma ya taka rawar gani wajen ayyukan kwamitoci, duk da cewa bai kai a zauren majalisar ba.[4]

A cikin shekara ta 2008 ne hukumar kula da iyakokin ƙasa da kwamitin tattara kuɗaɗen shiga da kuma rabon kuɗaɗen shiga suka miƙa ragamar tafiyar da rijiyoyin mai da ke cikin tekun Bakassi daga jihar Cross River zuwa jihar Akwa Ibom. A cikin watan Yulin 2009, Gregory Ngaji ya ce: “Abin da waɗannan hukumomin biyu suka yi ya saɓa wa doka kuma za mu yi duk abin da zai sa mu dawo da rijiyoyin mai.[5]