Jump to content

Mary Akrami

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mary Akrami
shugaba


shugaba

Rayuwa
Haihuwa 20 century
ƙasa Afghanistan
Karatu
Makaranta University of Peshawar (en) Fassara Bachelor in Business Administration (en) Fassara
Sana'a
Sana'a Mai kare hakkin mata
Kyaututtuka

Mary Akrami (Persian; 1975 ko ( 47-48) “Shugabar Cibiyar Bunƙasa Ƙwarewar Mata ta Afghanistan ce. Ta wakilci al’ummar farar hula na Afghanistan a taron Bonn na 2001. A shekarar 2003, Cibiyar Bunƙasa Ƙwarewar Mata ta Afghanistan ta buɗe mafakar mata ta farko a Kabul, Afghanistan. Mafakar tana ba da shawara ta doka, darussan koyo da rubutu, shawarwari na tunani, da horo na ƙwarewa ga mata masu buƙata. Akrami tana kan kira a kowane lokaci a mafakar, kuma ƙarƙashin jagorancinta wasu daga cikin matan sun yi Allah wadai da masu cin zarafinsu a fili kuma sun shigar da ƙara a kotu a kansu, wani abu da kusan ba a taɓa jin sa ba a Afghanistan a baya. Ta fuskanci barazanar rayuwa saboda aikinta.”. [1].[2] [3][2] .[1]..[1]

Ta sami lambar yabo ta Mata masu jarumta ta Duniya a shekara ta 2007 kuma an ambaci sunanta a cikin jerin mata 100 na BBC na shekara 2016 a matsayin ɗaya daga cikin mata masu ban sha'awa da tasiri a shekara.[1]