Jump to content

Kusada

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kusada

Wuri
Map
 12°28′00″N 7°59′00″E / 12.4667°N 7.9833°E / 12.4667; 7.9833
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jihohin NajeriyaJahar Katsina
Labarin ƙasa
Yawan fili 390 km²
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
kusada

Kusada ƙaramar hukuma ce a Jihar Katsina a Najeriya. Hedkwatarta tana cikin garin Kusada.

Manyan ƙabilun garin su ne Hausawa da Fulani.

Manyan garuruwansa sun haɗa da: Dudunni, Dangamau, Yashe, Mawashi, Ƙofar Kaikai. Al’ummar ƙaramar hukumar Kusada, manoma ne da makiyaya. Rayuwarsu ta inganta domin tun da daɗewa, gwamnati ta samar musu abubuwan more rayuwa kamar, makarantu, asibitoci, titinan kwalta, rijiyoyin burtsatse (na hannu da masu amfani da hasken rana), rijiyoyin burtsatse na gonaki, madatsun ruwa, kasuwannin cikin gida da dai sauransu.

Duk makarantun sakandare da firamare na kwana da na je-ka-ka-dawo na gwamnati, suna cikin garin da wasu daga cikin manyan ƙauyukan ƙaramar hukumar. Haka nan kuma, ƙaramar hukumar na da gidaje na musamman na gwamnati, masallatan juma'a, kyawawan hanyoyin da fitattun layika.

Garin yana da faɗin murabba'i 390 tare da kuma yawan jama'a 199,267 2, kamar yadda ƙidayar shekara ta 2006 ta nuna.

Lambar gidan wayar yankin ita ce 833.

  1. https://web.archive.org/web/20121126042849/http://www.nipost.gov.ng/postcode.aspx